Masar zata jagoranci taron Libya
Kasar Masar zata jagoranci taron Ministocin harakokin wajen kasashen da ke makwabtaka da Libya game da rikicin kasar a ranar Litinin, bayan Mayakan sa-kai sun karbe ikon tashar jirgin sama a birnin Tripoli.
Wallafawa ranar:
Wannan matakin na zuwa ne bayan gungun Mayakan Fajr sun kwace ikon tashar jirgin sama a Tripoli.
Mahukuntan Libya sun kasa samar da zaman lafiya a kasar tun lokacin da ‘Yan tawaye suka kawar da gwamnatin Marigayi Kanal Ghaddafi.
Masar zata jagoranci taron ne a birnin al Kahira wanda zai kunshi ministocin harakokin waje na kasashen Libya da Masar da Algeria da Tunisia da Sudan da Chadi da Nijar.
A watan Yuli an gudanar da irin wannan taron inda ministocin harakokin wajen wadannan kasashen suka yi kira ga bangarorin siyasar Libya su hau teburin sulhu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu