Isa ga babban shafi
Najeriya

Jega: INEC ta shirya ma zaben Osun

Hukumar Zabe a Najeriya tace ta shirya tsaf domin gudanar da zaben Jihar Osun da za’a yi a karshen wannan mako. Shugaban hukumar Farfesa Attahiru Jega yace hukumar ta kuma kwashe lokaci mai tsawo tana cire sunayen mutanen da suka yi rajista fiye da daya a fadin kasar.

Shugaban Hukumar Zabe a Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Shugaban Hukumar Zabe a Najeriya Farfesa Attahiru Jega RFI/Bashir
Talla

A ranar Assabar ne 9 ga watan Agusta za’a gudanar da zaben gwamna a Jihar Osun inda Gwamnan Jihar mai ci Rauf Aregbesola na Jam’iyyar adawa ta APC ke neman wa’adi na biyu, kuma zai fafata ne da Dan takarar Jam’iyyar PDP mai mulki a Tarayya Iyiola Omisore.

‘Yan takara daga Jam’iyyu siyasa 20 ne zasu fafata a zaben na neman kujerar gwamna a Osun.

Jega yace hukumar zabe ta shirya domin gudanar da zaben Osun wanda suke fatar zai fi na Ekiti tsabta bayan sun inganta rijistar masu kada kuri’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.