Isa ga babban shafi
Najeriya

Ma'aikatar tsaron Najeriya na biciken kisan 'yan Shi'a a Zaria

Rundunar tsaron tarayyar Najeriya ta ce yanzu haka ta kaddamar da bincike akan zargin da jagoran mabiya Mazhabar Shi’a a kasar Sheikh Yakubu Ibrahim Al-zakzaky ya yi wa jami’an sojan kasar, da cewa suna da hannu wajen kashe magoya bayansa da kuma ‘yansa lokacin da suke zanga-zangar nuna goyon baya ga Palasdinu a juma’ar karshe ta watan Ramadan da ya gabata a garin Zaria.

Jagoran mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya El-Zakzaky
Jagoran mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya El-Zakzaky
Talla

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya jiyo kakakin rundunar tsaron kasar Manjo Janar Chris Olu-kolade na cewa binciken ya zaman wajibi domin kwantar da hankula.

Olukolade ya ce tuni rundunar sojan kasar mai kula da shiyyar da lamarin ya faru ta gudanar da binciken na farko, to amma duk da haka ana ci gaba da gudanar da bincike a babbar shalkwatar tsaron kasar domin tantance hakikanin abinda ya faru.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.