Isa ga babban shafi
Najeriya

“Muna son Jonathan ya kai ziyara Chibok”

Wasu Iyayen ‘Yan matan da Mayakan Boko Haram suka sace sun bukaci Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kai ziyara garin Chibok domin ganawa da dukkaninsu da aka sace ‘yayansu ba tare da nuna fifiko ba akan wasu.

Wasu iyayen 'Yan matan garin Chibok da aka sace a cikin  Jihar Borno a Najeriya
Wasu iyayen 'Yan matan garin Chibok da aka sace a cikin Jihar Borno a Najeriya Reuters/Stringer
Talla

Sama da watanni uku da aka shafe, da sace ‘Yan Mata 276 a wata Makarantar Sakandare a garin Chibok, amma har yanzu Shugaban Najeriya bai gana da ‘iyayen ‘Yan matan ba ko kuma wasu daga cikin ‘Yan matan 57 da suka tsere daga hannun Mayakan Boko Haram.

A ziyarar da ta kawo a Najeriya, Malala Yousafzai ‘Yar rajin tabbatar da ilimin ‘yaya mata da Mayakan Taliban suka harba, ta bukaci Goodluck Jonathan ya gaggauta daukar matakai domin kubutar da ‘Yan matan daga hannun mayakan Boko Haram.

Shugabannin Chibok sun ce sai idan Jonathan ya kawo ziyara a Chibok kafin su amince da gaske shugaban ya ke game da kokarin kubutar da ‘yayansu da aka sace.

Dauda Iliya daya daga cikin iyayen Chibok yace abin kunya ne ace sai da Malala ta kawo ziyara a Najeriya sannan Jonathan zai nemi ya gana da su.

Iliya yace ‘Yan mata 57 suka gudo yayin da 219 suka rage a hannun Mayakan Boko Haram, amma iyayen 9 daga cikinsu ne kawai aka ce ana son shugaban ya gana da su.

“Babu yadda za’a yi maka mutuwa kuma ka tashi ka tafi gaisuwa” inji Dauda Iliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.