Isa ga babban shafi
Najeriya

INEC ta yi tanadin na’urar magance magudin zabe

Hukumar zaben mai zaman kanta a Najeriya tace akwai wasu manyan kalubale da ke gabanta kafin zaben 2015. Hukumar tace ta tanadi wata na’ura da zata taimaka wajen dakile magudin zabe a Najeriya.

Shugaban Hukumar Zabe a Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Shugaban Hukumar Zabe a Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Talla

A tattaunawarsa da kafofin yada labarai na kasashen waje shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya Farfesa Attahiru Jega, yace barnar zabe a kasar ta yi yawa har ta yi kanta, bayan ya zayyana kalubalen da ke gabansu a zaben 2015.

Jega yace babban kalubale shi ne yadda ‘Yan siyasar Najeriya suka dauki zabe da zafi.

“idan da ‘Yan siyasa za su shigo al’amarin zabe da tsanaki da za’a iya warkar da matsalolin zabe kashi saba’in cikin dari”.

02:56

Rahoto: INEC ta yi tanadin na’urar magance magudin zabe

Jega ya yi watsi da masu rade radin cewar ba za’a iya gudanar da zaben shekara mai zuwa ba a Jihohin Borno da Yobe da Adamawa saboda matsalolin tsaron da Yankunan ke fuskanta.

Duk da akwai kalubale na Tsaro, amma Farfesa Jega ya tabbatar da zasu gudanar da zabe a Jihohin arewa maso gabaci guda uku da aka kafawa dokar ta-baci.

A jawabinsa Jega yace hukumar Zabe zata kara yawan muzabu da Jami’an zabe, tare da neman a yi wa sashen dokar zabe na 30 gyara da ke Magana game da zaben Dan takara saboda yadda ‘Yan siyasa ke sabawa matakan fitar da dan takara a jam’iyyarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.