Isa ga babban shafi
Najeriya

Shekau yace su suka kai harin Abuja da Lagos

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau yace su suka kai hare haren bom a biranen Abuja da Lagos a cikin wani sabon sakon bidiyo da ya aikawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa a yau Lahadi.

Abubakar Shekau Shugaban Kungiyar Boko Haram.
Abubakar Shekau Shugaban Kungiyar Boko Haram. As received by Reuters
Talla

A cikin sakon na tsawon minti 16, Shekau kuma yace su suka kai tawayen hare haren bom a garin Jos a watan Mayu da kuma harin da aka kai a wata kwalejin ayyukan Lafiya a Kano.

Abubakar Shekau yace su suka dasa bom da ya tashi a unguwar Wuse 11 a birnin Abuja a ranar 25 ga watan Yuni inda aka samu hasarar rayukan mutane 22.

A washegari ne kuma aka samu fashewa a Unguwar Apapa a Lagos yankin kudancin Najeriya, wanda mahukuntan Jahar suka ce ya faru ne sakamakon fashewar tunkunyar gas na dafa abinci.

Amma a cikin sakon bidiyon Shekau ya karyata ikirarin na mahukuntan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.