Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Mutanen Sudan ta Kudu suna kwarara zuwa Habasha

Majalisar Dinkin Duniya, ta nuna damuwarta kan irin mawuyacin halin da ‘yan gudun hijran kasar Sudan ta Kudu ke fuskanta, musamman ma abinda ya shafi batun abinci. Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce yanzu haka akwai akalla ‘yan gudun hijra kusan dubu dari da arba’in da bakwai a sansanonin da aka kafa a kasar Habasha da ke makwabtaka da Sudan ta Kudu.

Wani Yaro da ke fama da Amai da Gudawa kwance a gadon Asibiti a birnin Juba
Wani Yaro da ke fama da Amai da Gudawa kwance a gadon Asibiti a birnin Juba REUTERS/Andreea Campeanu
Talla

Kungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa nan da makwanni Kasar Sudan ta Kudu zata shiga matsanancin hali na yunwa idan har ba a yi gaggawar samar da agajin abinci ba.

Akwai kuma Kungiyoyin kare hakkin bil adama daga kasashe daban daban na duniya, da suka nuna damuwarsu kan yadda ake kashe fararen hula da kai hare hare kan jami’an hukumar da ke kula da yara ta UNICEF yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsalar tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.