Isa ga babban shafi
Nijar

An cafke wasu Matan ‘Yan siyasa a Nijar

Jami’an ‘Yan sandan kasar Nijar sun kama matan wasu ‘yan siyasan kasar biyu, da ake zargi da hannu a fataucin yara kanana daga kashen Nigeria da Benin, don sayar da su a Nijar. Ana zargin Mai dakin Shugaban majalisar dokokin kasar Hama Amadou, da kuma Uwar gidan ministan aikin gona Abdou Labo da hannu a badakalar.

Hama Amadou shugaban majalisar Dokoki a Nijar
Hama Amadou shugaban majalisar Dokoki a Nijar AFP PHOTO STEPHANE DE SAKUTIN
Talla

Sai dai lauyan mai dakin Hama Amadou, Maitre Sule Umaru ya musanta zargin, kuma a cewarsa an kama su ne ba tare da wata sheda ba akan laifin da ake tuhumar sun aikata.

Hukumar yaki da Fataucin Mutane a Najeriya NAPTIP tace ba ta da masaniya akan batun da ya shafi fataucin Yara zuwa Nijar.

Rahotanni daga Nijar sun ce ‘Yan sandan kasar sun cafke mutane kusan 17 da ake zargi suna fataucin jarirai daga Najeriya. Cikinsu kuma akwai Matar ministan noma da matan wani tsohon daraktan Banki da ke hannun ‘Yan sanda.

A Nijar dai akwai rikicin siyasa tsakanin ‘Yan adawa da shugaban kasa Mahamadou Issoufou.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.