Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Karshen yajin aiki kamfanonin hako ma'adinai a Afrika ta kudu

Masu hako ma’adinai a kasar Afrika ta kudu sun cimma yarjejeniya na kawo karshen yajin aiki a kasar, bayan da suka kwashe tsawon watanni ma’aikatan suna yajin aiki.Kungiyar hako ma’adinai ta AMCU dake wakiltar dubban ma’aikata ta sanar da cimma nasara wajen gani an kara kudaden da ake biyan ma’aikatan hako ma’adinan a kasar Afrika ta kudu.  

Shugaban kasar Afrika ta kudu Zuma  da  ma'aikantan  hako ma'adinai Afrika ta kudu.
Shugaban kasar Afrika ta kudu Zuma da ma'aikantan hako ma'adinai Afrika ta kudu. REUTERS/Stringer
Talla

A yau talata dinan ne kungiyar hako ma’adinai zata sanya hanu a takarda, wata hanyar kawo karshen rikicin.
Shugaban kungiyar Joseph Mathunjwa yace zasu amince da karamin albashi na tsawon shekaru uku akan kudin kasar Afrika ta kudu Rand 12,500.

Shawarar da manyan kungiyoyin da ke hako ma’adinan suka yi naam da ita.
Yajin aiki kungiyar hako ma’adinai a Afrika ta kudu ya haifar da dakatar da ayyukan hako ma’adinai, lamarin da ya gurgunta tattalin arzikin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.