Isa ga babban shafi
Najeriya-Sri Lanka

Boko Haram: Najeriya zata kwaikwayi Sri Lanka

Rundunar Sojan Najeriya tace tana nazarin bin dubarun da kasar Sri Lanka ta bi ta karya mayakan Tamil Tigers, domin share al’amarin ‘Yan kungiyar Boko Haram a kasar, bayan wata tawagar manyan Jami’an Sojin Sri Lanka sun kawo ziyara a Najeriya.

Kakakin rundunar Sojin Najeriya, Chris Olukolade.
Kakakin rundunar Sojin Najeriya, Chris Olukolade. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Cikin wata sanarwa da ta bayar, ma’aikatar Tsaron Najeriya tace ta gana da jami’an tsaron Sri Lanka kuma sun tattauna yadda za’a kulla zumuncin domin kawo karshen ayyukan Mayakan Boko Haram.

An shafe Shekaru ana yakin basasa a Kasar Sri Lanka kuma sai a 2009 ne kasar ta kawo karshen mayakan Tamil Tigers.

Amma Fasalin Sri Lanka na yakar ‘yan tawayen ya sha suka daga kasashen duniya saboda irin hasarar rayukan fararen hula da aka samu a tsawon shekaru 30 da suka fafata.

Wannan kuma na zuwa ne bayan Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gana da takwaransa na Pakistan Mamnoon Hussain akan yadda za su hada hannu domin yaki da ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.