Isa ga babban shafi
Nigeria

Addu'in zaman lafiya a Tarayyar Najeriya

A Najeriya, Maimartaba Sarkin musulmi Dr Muhammad Sa’ad Abubakar na 3, ya bukaci al’ummar musulmin kasar da hada karfi da karfi domin kawo karshen ayyukan kungiyar boko Haram wanda ke haifar da fitini a cikin al’umma sannan ake danganta hakan da addinin musulunci.  

Sultan Sa'ad Abubakar
Sultan Sa'ad Abubakar
Talla

Sultan Sa’ad Abubakar wanda ke gabatar da jawabi a lokacin gudanar da addu’o’I na musamman dangane da bala’o’in da wannan kungiyar ta haifar wa Najeriya a babban masallacin juma’a da ke Abuja a yau, ya ce musulunci bai taba amincewa da ta’addanci ba, saboda haka ya kamata musulmi su tashi tsaya domin kawo karshen ayyukan kungiyar.

Har ila yau sarkin musulmin wanda kuma shi ne shugaban Majalisar Koli ta Addinin Islama a kasar, ya bayyana halin da kasar ke ciki a yau da cewa ya fi yakin basasar shekarar 1967 zuwa 1970 muni.

An dai gudanar da wadannan addu’o’I ne a gaban dimbin jama’a da suka hada da manyan malaman addini, da mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo da kuma manyan sarakunan gargajiya na kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.