Isa ga babban shafi
Mali

Bankin Duniya ya jinkirta bai wa kasar Mali rancen kudi

Asusun lamuni na duniya IMF ya ce zai jinkirata bai wa kasar Mali rancen dalar Amurka milyan 6, domin gudanar da bincike dangane da wasu bayanai da ke cewa gwamnati za ta yi amfani da kudaden ne domin saya wa shugaban kasar sabon jirgi akan dala milyan 40.

Ibrahim Boubacar Keïta, shugaban kasar Mali
Ibrahim Boubacar Keïta, shugaban kasar Mali AFP PHOTO / HABIBOU KOUYATE
Talla

Mai magana da yawun asusun na IMF ya ce babbar manufar bai wa Mali rancen wadannan kudade shi ne domin yaki da talauci, amma ba domin sayen jirgin sama ba.

Mali dai kasa ce da ke farfadowa daga yakin basasa, lamarin da ya sa ta nemi taimakon kasashen duniya domin ceto tattalin arzikinta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.