Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane sun fara ficewa Borno

Rahotanni daga Maiduguri a Jahar Barno a Tarayyar Najeriya sun ce, mutane sun fara ficewa daga garin, saboda fargabar halin da za su iya samun kansu a ciki, bayan da kasashen duniya suka bayyana aniyar tura dakaru domin taimakawa wajen kubutar da dalibai ‘Yan mata sama da 200 da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su a garin Chibok.

Birnin  Maiduguri, da ke fama da hare haren Boko Haram a Jahar Borno a Najeriya
Birnin Maiduguri, da ke fama da hare haren Boko Haram a Jahar Borno a Najeriya Ben Shemang / RFI
Talla

Sama da makwakanni uku da suka gabata ke nan da ‘Yan bindiga suka sace Daliban Mata a wata Makarantar Sakandare a Jahar Borno.

A cikin wani sakon Bidiyo, Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau yace su suka sace matan kuma a cikin sakonsa yace zai sayar da Matan wadanda ya danganta a matsayin Bayi.

Furucin Shekau shi ne ya ja hankalin duniya inda manyan kasashe irinsu Amurka da Faransa da Birtaniya suka yi alkawalin taimakawa Najeriya domin kubutar da ‘Yan Matan.

Amma Isifu Manaja wani mazauni garin maiduguri, ya shaidawa RFI Hausa cewa mutane da dama sun fara ficewa daga Maiduguri saboda fargabar abinda zai faru idan Sojojin kasashen waje suka shigo yankin.

01:00

Ministan watsa Labaran Najeriya Labaran Maku

Ministan Watsa Labaran Najeriya Labaran Maku yace shigowar Sojojin na kasashen Waje ba yana nufin za a zo a yi yaki a Najeriya ba ne, kuma ba gwazawa ba ne daga Sojojin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.