Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: Jonathan ya nemi taimakon Amurka

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sha alwashin gwamnatinsa zata yi kokarin kubutar da mata daliban Makaranta 223 da ‘Yan bindiga suka sace a Chibok, tare da  neman agajin Amurka domin magance kalubalen matsalar tsaron da ke addabar Najeriya.

Shugaban Faransa, François Hollande a ziyarar da ya kawo a Najeriya
Shugaban Faransa, François Hollande a ziyarar da ya kawo a Najeriya REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Shugaban na Najeriya ya sha alwashin kubutar da daliban ne da aka sace a tattaunawar shi da wasu ‘Yan Jaridun Najeriya da aka yada kai tsaye a kafar Telebijin.

A cikin tattaunawar, shugaban na Najeriya yace sun tuntubi manyan kasashen duniya irinsu Faransa da Birtaniya da China da Amurka domin neman taimako.

A ranar 14 ga watan Afrilu ne aka sace Mata daliban Makaranta sama da 200 a garin Chibok da ke Jahar Borno.

Amma Jonathan ya danganta bacewar daliban a matsayin wani al’amari da ya shafi duniya baki daya, ta la’akari da bacewar jirgin Malaysia da ake ci gaba da nema a teku.

Shugaban yace zai hada kai da kasashen da Najeriya ke makwabtaka da su a kokarin gwamnatinsa na kubutar da matan da aka sace.

Tun lokacin da aka sace ‘Yan Matan, Gwamnatin Jonathan ke fuskantar suka daga ‘Yan Najeriya musamman watannin da aka kwashe yankin Jihohin arewacin kasar na cikin dokar ta-baci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.