Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya da Boko Haram sun aikata laifukan yaki-Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International tace jami’an tsaron Najeriya da kuma Mayakan Kungiyar Boko Haram sun aikata laifukan yaki tare da cin zarafin bil’adama a tashin hankalin da ake fama da shi yankin arewa maso gabacin kasar.

Sojojin Najeriya da ke farautar mayakan Kungiyar Boko Haram
Sojojin Najeriya da ke farautar mayakan Kungiyar Boko Haram AFP/Quentin Leboucher
Talla

Amnesty tace a cikin watanni uku da suka gabata, a shekarar 2014, an kashe mutane fiye da 1,500 a Najeriya.

A kwanan baya, Hukumar agajin gaggawa ta NEMA tace mutane sama da 1,000 ne aka kashe a 2014, kuma sama da mutane 250,000 suka kauracewa gidajensu. A watan Maris din nan Hukumar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch tace mutane 700 suka mutu a Najeriya a 2014.

Amnesty tace yawancin wadanda ake kashewa fararen hula ne.

Rahoton, kamar yadda Netsanet Belay shugabar Sashen bincike kan al’amurran da suka shafi Nahiyar Afirka a kungiyar ta Amnesty International ke cewa, ya dogara ne da tattaunar da jami’anta suka yi da mazauna yankunan da lamarin ke faruwa, da lauyoyi da wakilan wasu kungiyoyi na kare hakkin bil’adama.

Rahoton yace a ranar 14 ga watan Maris, lokacin da ‘yan Boko Haram suka kai hari a barikin sojan Giwa da ke Maiduguri tare da ‘yantar da magoya bayansu, sojojin sun mayar da martani tare da kashe mutane sama da 600 a wannan rana kawai, kuma daga cikin wadannan mamata ba wanda ke dauke da makami.

Wani shaidun ganin da ido ya bayyana wa kungiyar ta Amnesty cewa, yana kallo jami’an tsaro suka jera mutane 56 daga cikin mutanen da suka yi yunkurin tserewar a cikin wani dakin makaranta, ya kuma ji mutane na ihu suna cewa “mu ba ‘yan Boko Haram ba ne’’ amma a gabansu sojoji suka tara mutanen sannan suka bindige su har lahira a wani fili da ke bayan jami’ar Maiduguri.

Kungiyar ta ce yanzu haka akwai wasu manyan kaburbura guda uku da aka haka a sassa daban daban dauke gawarwakin mutane a birnin Maiduguri.

Amnesty ta bayyana wadannan kashe-kashen a matsayin laifukan yaki da kuma cin zarafin bil’adama, wadanda ya kamata Majalisar Dinkin Duniya, da Kungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS, su taimaka wa Najeriya domin gudanar da bincike kan wannan lamari.

Kungiyar tace wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ake shirin mika ragamar jagorancin Kwamitin tsaro da zaman Lafiya na Kungiyar Tarayyar Afirka a hannun Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.