Najeriya ta bude kofar tattaunawa da Boko Haram
A wata Ziyara da ya kai a garin Maiduguri, Babban hafsan rundunar Sojin Najeriya Laftanal Kanal Kenneth Minimah yace kofar tattaunawa da mayakan Boko Haram a bude take kamar yadda zasu iya yin amfani da karfi domin murkushe su.
Wallafawa ranar:
Minimah ya fadi haka ne a lokacin da ya kai ziyara a Barikin Sojoji inda Mayakan Boko Haram suka kai hari domin jajantawa tare da karfafawa Sojoji kwarin gwiwa.
Akwai dai kwamitin da shugaba Goodluck Jonathan ya kafa domin tattaunawa da Boko Haram don kawo karshen kashe kashen rayukan mutane a Najeriya. kodayake shugaban Kungiyar ya fito a faifan Bidiyo yana yin watsi da tayin na sulhu
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu