Isa ga babban shafi
Algeria

An cafke masu zanga-zangar adawa da Bouteflika na Algeria

Kafafen yada labaran kasar Algeria, sun ce jami’an tsaron kasar sun cafke mutane fiye da 100 wadanda suka shiga zanga-zangar nuna adawa da sake tsayawar shugaba Abdul’aziz Bouteflika takarar neman mukamin shugabancin kasar karo na hudu.

Masu zanga-zangar adawa da takarar Bouteflika
Masu zanga-zangar adawa da takarar Bouteflika REUTERS/Ramzi Boudina
Talla

A jiya alhamis dimbin jama’a ne suka shiga wannan zanga-zanga don nuna rashin amincewa da tsayawar shugaban a zaben na watan Afrilu, inda suke cewa ba ya da koshin lafiyar da zai ba shi damar ci gaba da mulkin kasar.

Bouteflika wanda ya sha fama da rashin lafiya, kuma wan ya kwashe tsawon shekaru 15 yana shugabanci a Algeria, ya mika takardarsa ta neman shiga jerin ‘yan takara a zaben da za a yi a cikin watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.