Isa ga babban shafi
Najeriya

Sanatoci 11 sun canza sheka daga PDP zuwa APC a Najeriya

‘Yan majalisar Dattijan Najeriya 11 sun mika takardarsu ta canza sheka daga Jam’iyyar PDP mai mulki zuwa Jam’iyyar adawa ta APC zuwa ga shugaban Majalisa, a wata sabuwar baraka ga shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Tsohon Gwamnan Jahar Gombe Danjuma Goje
Tsohon Gwamnan Jahar Gombe Danjuma Goje
Talla

Sanatocin sun mika takardarsu ne ga David Mark inda a cikin wasikar suka ce sun fice PDP zuwa APC.

“Mun lura da abinda ke faruwa a Najeriya na tashin hankali da talauci” inji Tsohon Gwamnan Gombe Danjuma Goje daya daga cikin Sanatocin da suka fice PDP.

Sanata Goje yace sun fice PDP ne don sun lura akwai bukatar samun shugabanci na gari domin warware matsalolin Najeriya.

02:53

Sanata Danjuma Goje Tsohon Gwamnan Jahar Gombe

Bashir Ibrahim Idris

Dukkanin Sanatocin da suka canza sheka dai suna wakiltan arewacin Najeriya ne
Idan kuma David Mark ya amince da matakin Sanatocin 11 na canza sheka hakan zai rage yawan Sanatocin da PDP ta ke da su a babbar majalisar zuwa 62 cikin 109.

A ranar 19 ga watan Disemba wasu ‘Yan majalisar Wakilai suka fice PDP zuwa APC wanda ya gurgunta rinjayen PDP a karamar Majalisa.

Kuma wannan dambarwar canza sheka a majalisar ta biyo bayan wasu gwamnoni guda 5 da suka fice Jam’iyyar PDP zuwa APC domin karya kudirin Shugaban kasa Goodluck Jonathan na neman wa’adin shuganaci na biyu.

Har yanzu dai shugaba Jonathan bai fito ya bayyana kudirin sake tsayawa takara ba wata kila saboda barakar da ya ke fuskanta a Jam’iyyarsa ta PDP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.