Isa ga babban shafi
Najeriya

APC ta koma PDP, inji Bafarawa bayan ya canza sheka

Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Alh Dalhatu Bafarawa, tare da magoya bayansa a kananan hukumomi 23 na Jihar, da wasu 'Yan tsohuwar Jam’iyyar ANPP da CPC sun fice daga Jam’iyyar gamayyar 'Yan adawa ta APC zuwa Jam’iyyar PDP mai mulki a Najeriya.

Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Alh Attahiru Bafarawa
Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Alh Attahiru Bafarawa Bioreports
Talla

Wannan ya zama al’ada ga ‘Yan Siyasar Najeriya na rashin rike akida da kuma saurin canza sheka daga wata jam’iyyar Siyasa zuwa wata.

“APC mun zo mun samu kan mu a cikin wani hali na kaka-ni-kayi, Gwamnoni sun shigo sun ce suna son shugabanci” a cewar Bafarawa a lokacin da ya ke bayyana dalilan da ya sa ya fice zuwa PDP.

01:34

Rahoto: Bafarawa ya canza sheka zuwa PDP

Faruk Yabo

Bafarawa yace ya amsa kira ne daga magoya bayansa musamman daga Sokoto da suka ce ba zasu iya tafiya da gwamnan Jahar ba na yanzu wanda ya dawo Jam’iyyar APC daga PDP.

A ranar Lahadi akwai dinbim mutanen Sokoto da suka fito a garin Bodinga domin nuna goyon bayansu ga Tsohon gwamnan na Sokoto.

Bafarawa ya taba tsayawa takarar shugaban kasa karkashin tutar Jam’iyyar ACN daya daga cikin Jam’iyyar da suka dunkule waje daya suka koma APC.

Tuni dai bangaren Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko suka mayar da martani.

“Rashin shigowar Dan Majalisar Jaha guda ya fi hasara gare mu bisa ga ficewar Bafarawa” inji Inuwa Abdulkadir shugaban riko na Jam’iyyar APC a Jahar Sokoto.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.