Isa ga babban shafi
Najeriya

Aliyu Gusau yana cikin sunayen Ministocin da Jonathan ya mika wa Majalisa

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya mika sunayen sabbin ministoci ga Majalisar Dattawan kasar domin amincewa da su. Cikin wadanda aka mika sunayensu, akwai Janar Aliyu Gusau daga Zamfara da Musiliu Obanikoro daga Lagos da Aminu Wali da Jamila Salik daga Kano da Mohammed Wakil daga Borno da Abdul Jelili Oyewale Adesiyan daga Osun.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Reuters/Tiksa Negeri/Files
Talla

Sauran sun hada da Dr Halliru Alhassan daga Sokoto da Boni Haruna daga Adamawa da Asabe Asma’u Ahmed daga Niger da Akom Etim daga Akwa Ibom da Lawrencia Laraba daga Kaduna, da Tamuno Danagogo daga Jihar Rivers.

Ana sa ran Janar Aliyu Gusau za'a ba mukamin kujerar ministan tsaro inda yanzu Labaran Maku Ministan yada labarai ke kula da sha'anin ma'aikatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.