Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan ya aika wa Obasanjo da wasikar martani

Shugaban Tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan, ya mayarwa Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da Martani a game da wasikar gazawar shugabanci da ya rubuta masa ranar 2 ga Disemba inda a cikin wasikar Jonathan ya kare kansa tare da musanta zarge-zargen da Obasanjo ya yi masa.

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a lokacin da ya ke jagorantar yakin neman zaben Jonathan a zaben 2007 a garin Abuja birnin Tarayya.
Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a lokacin da ya ke jagorantar yakin neman zaben Jonathan a zaben 2007 a garin Abuja birnin Tarayya. REUTERS/Sunday Aghaeze
Talla

Shugaba Jonathan ya rubutawa Obasanjo Wasikar martanin ne ranar 20 ga Disemba mai yawan shafi 16, kuma shugaban ya zana dililai guda 10 da suka zama wajibi ya mayar wa tsohon shugaban da martani.

A cikin wasikar, Jonathan ya bayyana irin rawar da Obasanjo ya taka a lokacin yakin neman zaben shi, yana mai danganta wasikar Obasanjo a matsayin babbar barazana ga sha’anin tsaro.

Jonathan ya kimanta darajar Obasanjo wanda yace mutum ne mai muhimmin matsayi a Najeriya domin ko ba komai ya mulki kasar a mulkin Soja da kuma na dimokuradiyya har na tsawon shekaru fiye da 11.

Wasu dalilan da Jonathan yace ya zama wajibi a gare shi ya mayarwa tsohon shugaban kasar da martani sun hada da yadda da ganga-gangan Obasanjo ya bai wa duniya damar sanin abinda ke cikin wasikarsa a daidai lokacin da kakakin Majalisar wakilai ta Tarayya ke zargin gwamnati Jonathan da gazawa wajen tunkarar rashawa da ta yi wa kasar katutu, yayin da shi kuma gwamnan babban Bankin kasar ke zargin kamfanin mai na NNPC da kin zubawa asusun Tarayya kudi fiye da dala bilyan 48 na tallafin Fetir, abin da Jonathan a cikin wasikarsa ke kallo tamkar hadin baki a tsakanin wadannan mutane.

A game da batun matsalar tsaro musamman rikicin Boko Haram, Jonathan ya mayar da martani a wasikarsa yana mai cewa matsalar ta samo asali ne tun 2002, inda yace yana daukar matakai da kuma samarwa jami’an tsaro kayan aiki domin shawo kan matsalar.

Jonathan ya karyata zargin da tsohon shugaban kasar ya yi na cewa gwamnati mai ci ta tsara kashe wasu masu hamayya da ita a fagen siyasa, yana mai cewa a tarihin Najeriya an san gwamnatocin da suka saba kashe masu hamayya da su amma ba Jonathan ba.

A batun yaki da rashawa Jonathan ya maryar wa Obasanjo da martani ne da wakokin da Fela ya rera masa a zamanin mulkin shi.

Shugaban na Najeriya a cikin wasikarsa ya rika kiran Obasanjo da suna Baba, tare da bayar da umurnin gudanar da bincike akan jerin zarge-zargen da Obasanjo ya rubuta masa wadanda Jonathan ya danganta tamkar cin mutumci.

Wadannan musayar kalamun tsakanin Jonathan da Obasanjo na zuwa ne a lokacin da Jam’iyyarsu ta PDP mai mulkin kasar ke fama da rikicin cikin gida, inda wasu gwamnonin arewacin kasar da ‘Yan majalisar wakilai 37 suka canza sheka zuwa Jama’iyyar gamayyar ‘yan adawa ta APC.

Akwai kuma tawagar shugabannin APC da suka kai wa Obasanjo ziyara a gonarsa da ke Ota da suka hada da Tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da Tsohon Gwamnan Lagos Bola Ahmed Tinubu da wasu gwamnoni da ke adawa da Jonathan.

Wani dalilai da Jonathan ya bayyana a cikin wasikar martani da ya aikawa Obasanjo, ya zargi Tsohon shugaban da kokarin haifar masa da kiyayya tsakanin mambobin Jam’iyyarsa ta PDP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.