Isa ga babban shafi
Najeriya-Amnesty

Amnesty ta bukaci Jonathan ya yi watsi da dokar haramta auren jinsi

Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty Internatonal ta yi kira ga shugaban Najeriya ya yi watsi da dokar haramta auren jinsi guda bayan dokar ta samu amincewar ‘Yan Majalisa inda ya rage shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sa hannu.

Kungiyoyin sun fito suna adawa da Auren jinsi a kasar Uganda
Kungiyoyin sun fito suna adawa da Auren jinsi a kasar Uganda Reuters
Talla

Tun a watan Mayu ne majalisar wakilai da Dattijai suka amince da dokar haramta auren jinsi guda a Najeriya inda dokar kuma ta hada da hukunta duk ‘Yan luwadi da ‘Yan madigo da aka kama suna mu’amula a bainar Jama’a.

Yanzu Shugaban kasa goodluck Jonathan ya rage ya sa hannu ga dokar domin haramta aure jinsi a Najeriya.

Aster van Kregten, Babban Jami’in kungiyar Amnesty a Afrika ya yi kira ga Shugaban ya yi watsi da dokar.

A ranar Juma’a ne ‘Yan majalisar Uganda suka amince da dokar hukuncin daurin rai da rai ga mutanen da aka kama suna madigo ko luwadi amma sai shugaba Yoweri Museveni ya amince da dokar.

Al’ummar mutanen Najeriya yawancinsu Musulmi ne da Kirista wadanda dukkanin addinan biyu sun la’anci auren jinsi guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.