Isa ga babban shafi
Najeriya

APC ta samu rinjaye a Majalisar wakilai bayan ‘Yan majalisa 37 sun fice PDP

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya rasa rinjaye a majalisar wakilai bayan da ‘Yan majalisu daga Jam’iyyarsa ta PDP 37 suka canza sheka zuwa sabuwar Jam’iyyar gamayyar ‘Yan adawa ta APC, wanda wannan wata sabuwar baraka ce ga shugaban.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a lokacin da ya ke zantawa da kamfanin Dillacin Labaran Reuters a fadar shugaban kasa.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a lokacin da ya ke zantawa da kamfanin Dillacin Labaran Reuters a fadar shugaban kasa. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Majalisar Wakilai tana da Mambobi 360 ne a Najeriya kuma yanzu Jam’iyyar PDP da ke da rinjaye tun dawowa mulkin demokuradiya a 1999 an bar ta da kujeru 171 bayan da ‘ya’yan Jam’iyyar 37 suka fice.

A martanin PDP, Jam’iyyar tace matakin na ‘Yan majalisun tamkar cin amanar mutanen yankunansu ne da suka zabe su karkashin tutar PDP.

‘Yan majalisun sun ce matsalolin da suka dabaibaiye jam’iyyar ne dalilian da ya sa suka canza sheka zuwa APC.

“Rashin kula da ‘Yan Jam’iyya da rashin gaskiya da amana na PDP shi ne dalilin da ya sa muka koma APC saboda kila zamu iya samun adalci”, a cewar Hon Mustapha Dawaki daya daga cikin, ‘yan majalisar da suka canza sheka.

Wannan dai wata sabuwar baraka ce ga Jonathan wanda ke kokarin daidaita Jam’iyyar PDP kafin zaben 2015 bayan ficewar wasu gwamnonin Jam’iyyar zuwa APC a watan jiya.

Har yanzu dai Goodluck Jonathan be fito ya bayyana kudirin zai yi tazarce ba amma take-taken Jam’iyyarsa ta PDP da rikicin da ya shafi Jam’iyyar ya nuna shugaban zai tsaya takara a zaben 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.