Isa ga babban shafi
Ilimi Hasken Rayuwa

Barayi da 'Yan damfara a Intanet

Wallafawa ranar:

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya diba matsalar 'Yan damfara da barayi masu satar kudade da bayanai ta hanyar Kwamfuta da Intanet. Wani sakamakon bincike na Kamfanin Norton, yace adadin kudaden da ake sacewa ta hanyar Intanet a duniya sun kai kudi Dalar Amurka Biliyan 113 kuma binciken yace adadin ya kai ace duk mutum guda cikin wadanda aka sacewa kudaden, an saci kudinsu da suka kai Dalar Amurka 300.

Barayin Intanet da 'Yan damfara
Barayin Intanet da 'Yan damfara Reuters
Talla

Rahoton yace a kasar Canada ne satar ta fi kamari inda aka saci kudaden mutane da suka kai Dala Biliyan uku a bara, kasa da adadin da aka sata a shekarar baya.

A cikin Rahoton na Norton an bayyana cewa wannan matsalar yanzu ta zama ruwan dare a kasashe da dama, kuma yawanci mutane sukan ci karo da hare hare daga barayin na Intanet.

Akwai dai Dubaru da kuma hanyoyi da 'Yan damfarar ko barayin na Intanet ke bi domin kai wa ga mutane don cim ma bukatunsu.

Wata hanya ita ce ta aiko da Sakwanni ga masu Mu'amula a shafin zumunta na Facebook kuma sakwannin sun kun shi kalaman soyayya dauke da hotunan mata da ke neman kulla kawance da mutum.

Akwai kuma hanyar da 'Yan Damfara ke bi domin cim ma mutane ta hanyar adreshinsu na Email. Wata hanyar kuma ita ce ta aiko da sako a wayar Salula da Lamba mai alamar kari, kuma irin wannan idan mutum ya kira lambar kafin ya ankara an tsame kudinsa.

Samun yawaitar amfani da wayoyi kirar Smartphones ya kara haifar da yawaitar wannan matsalar saboda damar da ci gaban fasaha ya samar ga masu amfani da salula domin mu'amular cinikayya ta hanyar cira da tura kudi a bankuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.