Isa ga babban shafi
Guinea

Ba za mu saurari korafi ba sai an kammala kidaya – hukumar zaben Guinea

Hukumar zabe a kasar Guinea ta ce sakamakon zaben ‘Yan Majalisun da aka yi a kasar zai dauki dogon lokaci kafin a sanar da shi, abinda ya sa ‘Yan adawar kasar suka fara gargadi kan cewar ba za su amince da duk wani magudi ba.

Masu kidayar kuri'u a Guinea
Masu kidayar kuri'u a Guinea AFP /Issouf Sanogo
Talla

Mataimakin shugaban hukumar, ElHadj Ibrahim Kalil Keita ya ce dama dokar zaben kasar ta bada damar sanar da sakamakon sa’oi 72 bayan kammala karbar sakamako, inda ya ke cewa ya zuwa yanzu wasu sakamakon ba su isa hukumar ba, saboda matsalar sufuri.

“Idan ahr su ‘yan adawan na da wani sakamamon zabe da za su nuna, mu bamu san da shi ba.” Inji Lauyan hukumar, Amadou Kebe.

Kebe ya kara da cewa har sai sun sami cikakkane sakamako sannan za su saurari korafe korafe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.