Isa ga babban shafi
Guinea Conakry

An dage zaben ‘Yan Majalisa a Guinea Conakry

An dage gudanar da zaben ‘Yan majalisar dokokin kasar Guinea Conakry daga gobe talata zuwa ranar 28 ga wannan wata na Satumba. Manzo na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Yammacin Afrika Sa’id Jinnit ya ce an dage zaben ne domin bai wa hukumar zaben kasar damar aiwatar da wadansu sauye-sauye.

Zabe a kasar Guinea Conakry
Zabe a kasar Guinea Conakry Olivier Rogez/RFI
Talla

A cewar Jami’in, Babban abin da ya fi damuwar wakilan kasashen duniya, shi ne yin gyara ga kura-kuran da aka gano dangane da yadda ake shirya wannan zabe. Yana mai cewa Sabado haka ne hukumar zaben kasar ta amince da sabbin sauye sauyen da kuma aiwatar da su a cikin gaggawa.

Sabbin bukatun da aka shata domin cim ma gudanar da zaben sun hada da:

-Datse yawan rumfunan zaben da ake da masu jefa kuri’a da yawansu ya fi dubu daya.

-Kara yawan jami’ai da kuma kayan aiki a dukkanin rumfunan zabe da ake da masu jefa kuri’u dari da yawansu ya kai 700 zuwa dubu daya.

-Matso da rumfunan zabe zuwa kusa da jama’a domin sauwaka masu wajen jefa kuri’unsu.

-Sannan na hudu kuma na karshe, hade kananan rumfuna zaben da ake da masu jefa kuri’un da yawansu bai taka kara ya karya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.