Isa ga babban shafi
Masar

Magoya bayan Morsi suna nan kan bakarsu a Masar

Magoya bayan hambararren shugaban kasar Masar Mohammed Morsi sun tsaya akan bakar su na lalle sai an dawo da Morsi saman madafan iko bayan sun gana da wakilin Amurka domin kawo karshen rikicin kasar.

Hoton Mohamed Morsi, wanda Sojoji suka tumbuke daga shugabancin Masar
Hoton Mohamed Morsi, wanda Sojoji suka tumbuke daga shugabancin Masar REUTERS/Asmaa Waguih
Talla

Bayan ganawa da mataimakin sakataren harakokin wajen Amurka William Burns, Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi ta Brotherhood sun ce sun tsaya ne akan tafarkin doka, har sai an dawo da zababben shugaban kasa tare da maido da kundin tsarin mulki da babbar majalisar kasar ta Shura.

Ziyarar Jami’in na Amurka na zuwa ne bayan Catherine Ashton ta Tarayyar Turai da Westerwelle, na Jamus sun kawo ziyara a Masar domin shiga tsakanin rikicin kasar.

Tun bayan bayan hambarar da gwamnatin Morsi a ranar 3 ga watan Yuli ne magoya bayan shi ke zanga-zangar neman dawo da shi ga mukamin shi na shugaban kasa.

Rahotanni sun ce a daren Assabar Babban hafsan Sojan kasar day a hambarar da Morsi ya gana da bangaren ‘Yan uwa musulmi domin warware takaddamar da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.