Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Al'ummar Zimbabwe suna kada kuri'ar zaben shugaban kasa

Yau ne alummar kasar Zimbabwe da yawansu ya kai milyan 6 da dubu 400 ke zaben Shugaban kasa da kuma na ‘yan majalisa, inda Shugaba mai ci Robert Mugabe ke karawa da Praiminista Morgan Tsvangirai.

Hoton 'yan takara a kasar Zimbabwe
Hoton 'yan takara a kasar Zimbabwe REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Yanzu haka dai duniya ta sa idanu taga yadda zaben zai gudana, yayin da jam’iyyar adawa ta MDC wadda ta tsayar da Morgan Tsvangiray takara, ke zargin cewa shugaba Mugabe da magoya bayansa na shirin tafka magudi a zaben.

To sai dai a jajibirin wannan zabe, Mugabe ya ce matukar dai ya fadi a zaben, to zai mika ragamar mulki ga wanda ya yi nasara.

Shugaba Mugabe mai shekaru 89 ya fada a fili cewar ya zama wajibi ga duk wanda ya fadi zaben da ya rungumi kaddara.

Ita ma dai kasar Amurka ta maganta akan yanda zaben zai gudana, kuma Maorgan Tsvangirai wanda a aka tilastawa fita daga cikin jerin ‘yan takara a shekarar 2008 bayan kisan da aka yiwa wasu jerin magoya bayan sa 200, ya shaidawa kafar Talabijin ta CNN cewar ya karbi Alkawarin da Mogabe yayi da kaifi.

A wani labarin kuma a lokacin da yake jefa kuri’ar sa a yau dinnan Piraiministan klasar Zimbabwe Morgan Tsvangirai ya bayyana cikakkiyar fatar cewar zai lashe zaben, tare da kada shugaban kasa Robert Mogabe.

Yace jefa kuri’ar babban abin Tarihi ne ga daukacin ‘yan kasar. Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake bada Rahotannin da ke nuna cewar an dan samu tashe tashen Hankulla a wasu sassan kasar sakamakon zaben dake gudana.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.