Mutane 4 sun mutu a yankin Kidal arewacin Mali
Rahotanni daga kasar Mali na cewa mutane Hudu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu raunuka, lokacin da rikicin ya barke tsakanin Azbinawa jar fata da kuma sauran al’ummomi bakar fata a garin Kidal da ke arewacin kasar, yayin da wasu rahotannin ke cewa an kona babbar kasuwar garin.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa a dai dai lokacin da mahukuntan kasar ke shirye shiryen zaben shugaban kasa bayan kwato arewacin kasar daga hannun ‘Yan tawaye.
Ma’aikatar tsaron kasar Mali ta tabbatar da faurwar lamarin, inda ta ce an kona gidaje da kadarori da dama a wannan gari da ake kallo a matsayin babban sansanin kungiyar ‘yan tawayen da ke neman kafa kasar azbinawa wato MNLA.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu