Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar za ta fuskanci sabbin hare hare, inji Mayakan da suka kai harin Agadez

Mayakan Algeria da suka yi ikirarin daukar alhakin kai hari a arewacin Nijar da ya janyo hasarar rayukan mutane 20, sun sake aiko da gargadin kaddamar da sabbin hare hare a kasar har sai Nijar ta janye dakarunta daga Mali.

Hoton harin Agadez da aka nuna a gidan Telebijin na kasar Nijar
Hoton harin Agadez da aka nuna a gidan Telebijin na kasar Nijar AFP PHOTO/TELE SAHEL
Talla

“Zamu kaddamar da sabbin hare hare a Nijar”, inji Mayakan a cikin wata sanarwa da suka aiko a shafin Intanet. Kuma Mayakan sun gargadi Faransa da sauran kasashen da suke yaki a Mali.

Harin wanda shi ne na farko da aka kai a Nijar, amma Mayakan na Algeria sun ce idan har shugaba Mahamadou Issoufou bai janye dakarun kasar ba to za su ci gaba da kai hare hare.

Mokhtar Belmokhtar shi ne kwamandan Kungiyar wanda dakarun Chadi suka yi ikirarin sun kashe a Mali. Kuma mayakan kungiyar sune na biyu da suka fito suka yi ikirarin kai harin Agadez a kamfanin Areva mallakin Faransa.

Akwai kuma kungiyar MUJAO da ke yakin tabbatar da shari’ar Musulunci a Mali da suka fito suka yi ikirarin kai harin na Agadez.

Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian yace Dakarun Faransa sun kai dauki domin taimakwa wajen yaki da Mayakan da suka kai harin Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.