Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan ya ba da umarnin sakin ‘Yan kungiyar Boko Haram

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta saki daukacin matan da ake tsare da su har ma da wasu ‘ya’yan kungiyar Boko Haram da ake zargi da ayyukan ta’adanci, a wani mataki na bude kofar samar da zaman lafiya a Arewacin Najeriya.

Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan Reuters/Eduardo Munoz
Talla

Sanarwar da ta fito daga Ma’aikatar tsaron Najeriya na zuwa ne bayan kafa dokar ta baci a Jahohi uku a Arewa maso gabashin kasar domin farautar mayakan Boko Haram.

Kungiyar ta Boko Haram ta dade tana neman a sake mata ‘yan kungiyar na ta a matsayin wani matakin bude kofar tattaunawa.
Kungiyar ta dade tana zargin hukumomin Najeriya da kama mata da yara kanana.

“Wannan matakin sake wasu daga cikin ‘yan kungiyar, na daga cikin irin matakin fadada kofar tattaunawa da ‘yan kungiyar.” Inji sanarwar.

Rahotanni na nuna cewa wannan mataki har ila yau na daga cikin irin shawarwarin da kwamitin da aka nada domin tattaunawa da ‘yan kungiyar ta Boko Haram inda Shugaban kwamitin da aka nada na sasantawa da kungiyar, Hon. Tanimu Turaki ya ce sun mika bukatar da a yi haka ga fadar ta shugaban kasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.