Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta nisanta kanta daga alhakin sace Shettima Mongunu

Kungiyar Jama’atu Ahlus Sunnah Lid da’awati wal Jihad da ake kira Boko Haram ta nisanta kanta daga alhakin yin garkuwa da Shettima Ali Monguno, tsohon Ministan Mai a Najeriya, wanda yana cikin dattawan da ke shiga tsakanin sasanta gwamnati da kungiyar.

Wani Hoton Shettima ali Mungunu da aka hada da hoton Mayakan Kunhiyar Jama'atu Ahlis sunna Lid Da'awati wal Jihad
Wani Hoton Shettima ali Mungunu da aka hada da hoton Mayakan Kunhiyar Jama'atu Ahlis sunna Lid Da'awati wal Jihad vanguard nigeria
Talla

A ranar juma’a ne wasu ‘Yan bindiga suka sace Tsohon Ministan a birnin Maiduguri, kuma Rahotanni sun ce ‘Yan bindigar sun nemi a biya su kudi Amma daya daga cikin shugabannin kungiyar Boko Haram Aliyu Tashaku ya nisanta kan su da daukar alhakin kungiyar.

“Ni Aliyu Tashaku na tura sunan Shettima Munguno a cikin mutanen da muka amince da su domin ganawa da gwamnati, yaya za’a yi ace mutumin da muka yarda da shi ace kuma mun sace shi” a cewar Tashaku.

00:42

Aliyu Tishaku

Malam Tashaku yace wadanda suka sace Shettima da sunansu za su dauki mataki kuma Allah zai tona asirinsu.

Shettima Ali Monguno, mai shekaru 87, ya taba rike mukamin Ministan Mai a 1970 kuma ya taba rike mukamin shugaban kungiyar kasashe masu arzikin Man fetir ta OPEC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.