Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ba ta gamsu da mambobin kwamitin sasantawa ba

Kungiyar Jama’atu Ahlul Sunnah Lida’awati wal Jihad, da ake kira Boko Haram ta bayyana kwamitin da Gwamnmatin kasar ta kafa dan ganawa da ita, a matsayin makahon kwamiti.

Shugabbannin Kungiyar Jama'atu Ahlul Sunnah Lil da'awati wal Jihad
Shugabbannin Kungiyar Jama'atu Ahlul Sunnah Lil da'awati wal Jihad AFP PHOTO / YOUTUBE
Talla

A cewar kungiyar babu wadanda suka bayar da sunayen su, a matsayin wadanda za a sa a cikin kwamitin, wanda hakan bai gamsar da su ba.

Daya daga cikin shugabanin kungiyar, Aliyu Tashaku ya bayyana Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, Shiekh Abubakar Gero, Comrade Shehu Sani da Barrista Solomon Dallung, a matsayin wadansu daga cikin wadanda suke fatan gani a cikin Kwamitin.

Kungiyar ta kuma zargi gwamnatin Najeriya da rashin aiwatar da sharuddan da su ka gindiya, wadanda su ne za su bude kofar tattaunawar.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.