Isa ga babban shafi
Najeriya

An sake gano masana’antar sayar da Jarirai a jihar Abia dake kudancin Najeriya

Jami'an tsaro a tarayyar Najeriya sun sake bankado wata masana'antar renon Jarirai da kuma sayar da su a yankin kudancin kasar, inda ake ajiye yara Mata da suka isa haihuwa a kula da su, su haihu a kuma sayar da Jariran, a basu kudi su kuma sake daukar wani ciki. Akawi dai Maza da aka tanada domin saduwa da Matan domin Mace ta dauki ciki, kamar dai Dabbobi.

Masana'antar sayarda Jarirai a jihar Abia
Masana'antar sayarda Jarirai a jihar Abia
Talla

Bayannai sun tabbatar da cewar Matan da ke wannan sana’ar ‘Yan Mata ne da suka fuskanci matsala a gidajen su da musamman aka kora daga Gida sakamakon wata matsala da suka iya huskanta da Iyayen su

Kowace daga cikin wadannan Matayen dai kan yi renon Ciki ne ta haifar ta kuma sayar a kan kudi Naira dubu 100 daya idan Namiji ne, idan mace ce kuwa, akan sayar akan kudi Naira dubu 80.

Masu sayen Jariran kuwa, kan sayi Jinjiri daya ne daga wadannan ‘yan Matan kan Naira dubu 450 idan Namiji ne, ta Mace kuwa, Naira dubu 400.

A yayinda jami’an hukumar samar da tsaro ga ‘yan Kasa wato Civil Defence suka kai harin mamaye a Gidan da ake wannan Sana’a, sun samu akalla ‘yan Mata 32 masu juna biyu da ake renon Cikkunan su da manufar sayarwa.

Hakama an gano cewar Masana’antar nada Rajista da gwamnatin jihar ta Edo

Wata bakauya daga cikin Matan da ake ajiyewa suyi Ciki a sayar ta bayyanawa ‘yan Civil Defence wadanda suka taba kama Matar da ke ajiye wadannan ‘yan Matan cewar Matar Mijinta dan sanda ne, kuma shi ne yayi Ruwa-Tsaki ga fitar da ita ta kuma cigaba da wannan sana’ar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.