Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya na nazarin yi wa Boko Haram afuwa, MEND na barazanar kai hari

Gwamnatin Najeriya na tunanin yi wa kungiyar Jama’atu Ahlus Sunnah Lidda’awati wal-Jihad, da ake kira Boko Haram afuwa, don kawo karshen zubar da jinin da ake ci gaba da samu a Arewacin kasar.

'Yan Boko Haram na karanta sanarwa
'Yan Boko Haram na karanta sanarwa REUTERS
Talla

Shugaban kasar, Goodluck Jonathan ne ya sanar da haka, a lokacin da ya ke ganawa da wata tawagar Kungiyar Dattawan Arewacin kasar, a karkashin jagorancin Dan Masanin Kano, Dr Yusuf Maitama Sule da suka gana da shi.

Wannan sanarwa dai ta zo ne a daidai lokacin da kungiyar nan mai kiran kanta mai fafutukar ‘Yantar da Yankin Niger Delta, wato MEND, ta ce daga gobe juma’a za ta kaddamar da hare-hare dan mayar da martani kan hukuncin daurin da aka yi wa daya daga cikin masu taimaka ma ta wato Henry Okah, da wata kotun Afrika ta kudu ta yi.

Wata sanarwar da kungiyar ta rabawa manema labarai ta hannun Jomo Gbomo, ta ce za ta kaddamar da hare-haren ne saboda wata wasika ta karya da Gwamnatin Najeriya ta rubuta, wadda aka yi amfani da ita wajen daure Okah, inda ta ce tana bukatar Gwamnati ta tattauna da ita, kamar yadda take shirin tattaunawa da kungiyar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.