Isa ga babban shafi
Kenya

An bayyana Uhuru Kenyatta a matsayin sabon shugaban kasar Kenya

Bayyana Uhuru Kenyatta a matsayin sabon shugaban kasar Kenya ya biyo ne bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Kenya ta bayyana shi a matsayin zababben shugaban kasar Kenya, wannan ya biyo ne bayan tantancewa da adadin kuri’un da ko wane dan takarar shugabancin kasar ya sama, yanzu haka dai ana shirye-shiryen rantsar da sabon shugaban kasa wanda shine zai kasance shugaban kasa na 4 a kasar ta Kenya

Uhuru Kenyatta zababben shugaban kasar Kenya
Uhuru Kenyatta zababben shugaban kasar Kenya REUTERS/Noor Khamis
Talla

Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Kenya Ahmed Issack Hassan yace Kenyatta ya samu nasara da akalla kashi 50.03% cikin 100% dan haka sakamakon ya nuna cewar babu bukatar a je zagaye na biyu na zaben.

Kenyatta dai ya samu adadin kuri’u 6,173,433 daga cikin kuri’u 12,338,667 da aka jefa, a yayinda Raila Odinga ya samu kuri’u 5,340,546 abinda ya bashi nasarar samun akalla kashi 43.28% cikin 100.

Amma mai Magana da yawun Piraiminister mai barin Gado wato Raila Odinga yace akwai yiyuwar Odinga zai kalubalanci sakamakon zaben a gaban Kuliya

Sai dai rahoton baya-bayan nan na nuna cewar Kenyatta ya amince da karban mukamin shugaban kasar ta Kenya

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.