Isa ga babban shafi
Tunisia

An kafa sabuwar gwamnati a kasar Tunisia

Pirimiyan kasar Tunisiya Ali Larayedh ya bayyana kafa sabuwar gwamnatin hadin guiwa bayan da aka cimma yarjejeniyar kai karshen rikicin Siyasar da kasar tayi fama dashi, tareda baiwa sabuwar gwamnatin tsarin aikin dake gabanta bayan da aka samu amincewar ‘yan tawaye da Jam'iyyun Adawa

Tutar kasar Tunisiya
Tutar kasar Tunisiya REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

Larayedh wanda mamba ne a cikin wata kungiya ta masu kishin Islama wato Ennahda ya bayyana a kafar Talabijin cewar a yau zai mikawa shugaban kasa jerin sunayen mambobin sabuwar gwamnati tare da sabbin tsare-tsaren ayukan dake gaban su.

Wannan Sanarwar dai ta zo ne akalla ‘yan Sa'o’I da yin wata tattaunawa bayan wani tashin hankalin da aka yi fama dashi, wanda kuma ya haifar da zub-da-Jinin al’umma a Watan daya gabata

Larayedh yace sabbin mutanen da zasu yi aiki da kuma aka tsamo daga Jam’iyyun Siyasa daban daban domin kulla Hadakar samar da cikakken ‘yanci, zasu sauka a karshen wannan Shekarar bayan an gudanar da zaben shugaban kasa dana ‘yan Majalisa

Yace an bada muhimman mukamai ne ga wadasu mutanen da al’ummar kasar suka sani da rikon gaskiya da Amana tsakanin masu kishin Islama da kuma bangaren Jam’iyyun Adawa

Yace Prosecutor Lotfi Ben Jeddou zai jagoranci Ma’aikatar kula da harkokin cikin Gida, sannan wani kwararre kan harkokin Diplomasiyya Othman Jarandi zai shugabanci Ma'aiaktar kula da harkokin waje, a yayinda Rachid Sabagh ya zama mai kula da Ma'aiaktar tsaro, aka kuma bada Ma’aikatar Shara’a ga Nadhir Ben Ammou.

Jam’iyyar ‘yan Uwa Musulmi ta bayyana a shafinta na Tweeter cewar yanzu mukamai 48 ne suka shiga Hannun Ennahda, tareda kula da akalla kashi 28 idan aka kwatanta da mukamai 40 da suke rike dasu a gwamnatin da aka wargaza.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.