Shugaban Mali ya yi watsi da matakin tattaunawa da Ansar Dine
Shugaban rikon kasar Mali Dioncounda Traore, ya yi watsi da matakin zama teburin sasantawa da Mayakan Ansar Dine da suka karbe ikon yankin Arewaci tsawon watanni Tara, amma shugaban ya ce a shirye ya ke ya tattauna da ‘Yan tawayen Abzinawa.
Wallafawa ranar:
Mista Traore ya shaidawa RFI cewa Gwamnatin shi a shirye ta ke ta shiga tattaunawa da wakilan Kungiyar ‘Yan tawayen Abzinawa ta MNLA, tare da watsi da duk wani matakin hawa teburin tattaunawa da Mayakan Ansar Dine.
Bayan karbe manyan biranen Arewacin kasar, Gao da Timbuktu da Kidal, Gwamnatin Faransa ta nemi a hau teburin tattaunawa da ‘Yan tawaye.
Kakakin ma’aikatar tsaron Faransa Philippe Lalliot, ya ce tattaunawa tsakanin Gwamnati da ‘Yan tawaye ita ce hanyar wanzar da zaman lafiya a Mali.
Amma Mista Traore yace zai iya tattaunawa da ‘Yan tawayen Abzinawa ba tare da Mayakan Ansar Dine ba wadanda ake alakantawa da kungiyar Al Qaeda.
A ranar 11 ga watan Janairu ne Faransa ta kaddamar da yaki a Mali domin kwato yankin Arewaci daga ikon Mayakan Ansar dine.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu