Isa ga babban shafi
Mali

Dakarun Faransa sun Kutsa kai Kidal, bayan karbe Gao da Timbuktu

Dakarun Faransa sun isa birnin Kidal, daya daga cikin manyan biranen da ke karkashin ikon ‘Yan tawaye a arewacin Mali. Wannan kuma na zuwa ne bayan dakarun Faransa sun karbe ikon biranen Gao da Timbuktu, makwanni uku da suka kaddamar da yaki domin kakkabe ‘Yan tawaye.

Dakarun Mali da Faransa a garin Timbuktu a arewacin Mali
Dakarun Mali da Faransa a garin Timbuktu a arewacin Mali REUTERS/Arnaud Roine
Talla

Dakarun Faransa suna fatar karbe ikon yankin arewaci kafin su mika ragamar tafiyar da tsaro ga dakarun Afrika.

Rahotanni daga Mali sun ce dakarun sun karbe ikon filin jirgin Kidal garin da ke da Nisan Kilomita 1,500 tsakani da Bamako babban birnin kasar Mali.

A watan Maris din bara ne Mayakan Ansar Dine da ‘Yan tawayen Abzinawa suka karbe ikon Arewacin Mali bayan Sojoji sun hambarar da gwamnatin farar hula kafin daga bisani ‘Yan tawayen Abzinawa suka balle daga kawancensu da ansar Dine saboda Shari’a.

Wasu Rahotanni sun ce Shugabannin Mayakan Ansar dine da Mayakan Al Qaeda reshen Maghreb sun fake a wani tsaunin Kidal da ke kan iyaka da Algeria da Nijar.

Dubban mutane ne aka ruwaito sun fice daga Kidal saboda matsalar ruwa da abinci.

Gwamnatin Amurka ta yi alkawalin daukar nauyin jigilar dakarun Afrika zuwa kasar Mali domin yaki da ‘Yan tawaye.

A Garin Timbuktu Rahotanni sun ce daruruwan mutane sun yi ta farafasa shaguna, suna kwasar ganima, wanda ba a dade da kwato shi daga hannun mayaka masu kishin Islama ba.

Mazauna birnin sun yi ta balle shagunan larabawa, da ‘yan kasashen Mauritania da Algeria, da suke zargin suna tallafawa mayakan da ake zargin suna da alaka da kungiyar Al-Qaeda.

Sai dai sojojin da suka karbe garin sun hana mutanen kwasar ganima.

Rahotannin na cewa an ci gaba da gudanar da harkokin rayuwa a birnin, bayan da Faransa ta jagoranci kwato shi daga hannu ‘yan tawayen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.