Isa ga babban shafi
Algeria-Mali

‘Yan Bindiga sun yi garkuwa da Turawa 41 a Algeria tare da kiran kawo karshen yaki a Mali

Sojojin Kasar Algeria, sun ce sun yi wa wasu ‘Yan bindiga Kawanya da suka yi garkuwa da mutane sama da 150 hadi da wasu ma’aikatan Kamfanin Mai ‘Yan kasashen waje sama da 40, bayan sun hallaka uku daga cikinsu.

Mokhtar Belmokhtar, Kwamandan Mayakan da suka yi garkuwa da Turawa a Algeria
Mokhtar Belmokhtar, Kwamandan Mayakan da suka yi garkuwa da Turawa a Algeria
Talla

Rahotanni sun ce, cikin ma’aikatan da aka yi garkuwa da su, akwai ‘Yan kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa da Norway.

A cewar Kamfanin Dillacin Labaran kasar Mauritania na Sahara Media da ANI, Mayakan sun kai hari ne domin mayar da martani ga Algeria saboda ba kasar Faransa damar amfani da sararin samaniyarta wajen kai wa ‘Yan tawayen Mali hari.

Mayakan kuma sun bukaci kawo karshen yaki a Mali kafin su mika mutanen da suka yi garkuwa da su.

Rahotanni sun ce Mayakan sun kai harin ne a Kamfanin Man Algeria na In Amenas wanda ke aikin hadin gwiwa da amfanin BP na Birtaniya da Kamfanin Statoil na Norway.

Daya daga cikin maharan, ya ce su magoya bayan kungiyar al qa’ida ne da suka samu nasarar tserewa daga Arewacin Mali zuwa Algeria bayan da Faransa ta kaddamar da hari a kansu.

Yanzu haka kuma Shugaban kasar Faransa François Hollande yace ya fara tattaunwa da mahukuntan Algeria game da batun garkuwa da Turawan.

Tsawon mako daya ke nan da faransa ta kaddamar da yaki a kasar Mali domin kakkabe Mayakan Ansar dine da suka karbe ikon yankin Arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.