Shugaban kasar Mali zai kai ziyara Faransa
Shugaban rikon kwarya na kasar Mali Diacounda Trarore na shirin kai ziyarar aiki a birnin Paris na kasar Faransa a ranar laraba ta makon mako mai zuwa domin ganawa da shugaba Francois hollande.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sa’o’i kadan kafin sanar da hakan ne dai shugaban na Faransa wanda ke gabatar da jawabi ga jami’an diplomasiyya na kasashen duniya a birnin Paris,ya bayyana cewa a shirye kasarsa take ta taimaka domin a yaki ‘yan tawayen kasar Mali matukar dai kwamitin tsro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da hakan.
Kawo yanzu dai babu karin bayani a game da muhimman abubuwan da shugaban na Mali da kuma na Faransa za su tattauna a kai, to amma ko shakka babu batun halin da ake ciki a arewacin Mali ne zai fi mamaye wannan ziyara ta shugaba Dioncounda Traore.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu