Isa ga babban shafi
MALI-AU-NATO

Tarayyar Afrika ta nemi taimakon NATO a rikicin Mali

Kungiyar Tarayyar Afrika ta nemi taimakon dakarun kungiyar tsaro ta NATO domin hada karfi wajen karbe arewacin Mali da ya fada hannun ‘Yan tawaye. Shugaban Kungiyar ne Boni Yayi, ya yi wannan kiran a lokacin da ya ke ganawa da manema Labarai a Canada.

Mayakan Kungiyar MUJAO a yankin birnin Gao arewacin Mali
Mayakan Kungiyar MUJAO a yankin birnin Gao arewacin Mali AFP PHOTO / ROMARIC OLLO HIEN
Talla

Shugaban ya bukaci taimakon kasashen duniya don magance rikicin kasar Mali, kafin ya watsu zuwa kasashen da ke Yankin.

Tun a watan Maris na bara kasar Mali ta rabu gida biyu bayan ‘Yan tawayen Abzinawa tare da Mayakan Ansar Dine sun karbe ikon yankin Arewaci.

Tuni dai Dakarun hadin gwiwar kasashen Afrika suka yi alkawalin karbe ikon yankin bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kudirin daukar matakin Soji.

Boni Yayi dai yace rikicin Mali ya shafi Duniya ne, don haka ya ke ganin ya dace Kungiyar NATO ta kawo gudunmuwarta.

Wasu kasashen kungiyar NATO da suka hada da Amurka da Faransa da Canada tuni suka amince su ba dakarun ECOWAS horo, amma har yanzu babu wata kasa daga cikinsu da ta cim ma wannan alkawalin.

Rahotanni daga Mali sun ce dakarun kasar Sun tunkari sansanin ‘Yan tawaye tare da harba Harsashen gargadi a kudancin kasar.

Wasu Rahotannin daga Jami’an tsaro na cewar ‘Yan tawayen sun hade kai a wani Sansani da ke Bambara Maoude kusa da birnin Timbuktu.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi kiran zama teburin sasantawa kafin daukar matakin soji a kasar Mali.

Masana kuma suna ganin rikicin Mali kan iya shafar kasashen da ke makwabtaka da kasar wajen kwararar makamai da ‘Yan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.