Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan yace za’a yi binciken musabbabin hadarin jirgin da ya kashe su Yakowa

A Najeriya, al’ummar Jahar Kaduna suna zaman makokin mutuwar Gwamnasu Patrick Ibrahim Yakowa, wanda ya mutu a hadarin jirgin sama mai saukar Angulu tare da tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara Janar Owoye Azazi da wasu manyan mutane guda Hudu a kan hanyarsu daga Bayelsa Zuwa Fatakwal.

Gwamnan Jahar Kaduna Patrick Yakowa da  Andrew Owoeye Azazi tsohon me ba Shugaban kasar Shawara game da sha'anin tsaro wadanda suka mutu a hadarin jirgin sama
Gwamnan Jahar Kaduna Patrick Yakowa da Andrew Owoeye Azazi tsohon me ba Shugaban kasar Shawara game da sha'anin tsaro wadanda suka mutu a hadarin jirgin sama Sturves
Talla

A wata Sanawar daga fadar shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bada umurnin gudanar da binciken abunda ya yi musabbiin faruwar hadarin.

Jirgin saman wanda mallakar Sojin Ruwan Najeriya ne, ya rikito kasa ne a kauyen Nembe a jahar Bayelsa da misalin karfe 3:30 na rana a jiya Assabar. Kuma an bayyana babu wanda ya rayu a cikin jirgin mai dauke da mutane Shida wadanda ke kan hanyarsu Zuwa jana'izar mahaifin Oronto Douglas.

Cikin wadanda suka suka mutu sun hada da Dauda Tsoho da Mohammed Kamal da kuma matukan jirgin, Kwamanda Murtala Mohammed Daba da Laftanal Adeyemi Sowole.

Batun hadarin jiragen sama dai ba bakon abu ba ne a Najeriya.

A baya bayan nan a watan Maris, wani karamin jirgin sama na 'Yan sanda dauke da wani babban jami'in 'yan sandan ya taba faduwa a garin Jos, inda mutane hudu suka mutu.

Wani jirgin fasinja mallakar kamfanin Dana ya fadi a watan Yuni, a jihar Legas, inda ya kashe mutane 163.

Haka kuma a watan Oktoba akwai hadarin jirgi da ya rutsa da gwamnan jahar Taraba Danbaba Suntai kodayake shi ne ke tukin jirgin da kan shi.

Yanzu dai Mataimakin Yakowa ne za’a rantsar a matsayin sabon gwamnan jahar Kaduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.