An sace tallafin ambaliyar ruwa a Nijar
Rahotanni daga Jamhuriyyar Niger na cewa an sace tallafin da gwamnatin kasar ta samu daga kasashen wajen domin tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa. Rahotannin na cewa wadanda gwamnatin ta daurawa alhakin raba Tallafin ga mutane, su ne suka sace kayyakin.
Wallafawa ranar:
Nijar ta samu tallafin abinci da ya kai Ton 6,300 daga kasashen waje bayan samun ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 68 tare da raba miliyoyin mutane da gidajensu a watan Agusta.
Ministan cikin Gida Abduo Labo shi ne ya tabbatar da haka a gaban manema labarai. Kodayake bai ce ga adadin abinda aka sace ba.
Jamhuriyyar Nijar dai na daya daga cikin kasashen Yankin Sahel da ke fama da matsalar karancin Abinci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu