Isa ga babban shafi
ECOWAS-Mali-Guinea Bissau

Hafsoshin Sojin ECOWAS zasu gana a Najeriya game da Guinea Bissau da Mali

A Yau Litinin ne Manyan Hafsoshin sojin kasashen Afrika ta Yamma zasu gudanar da wani taro a Abuja babban birnin Najeriya, don nazarin hanyoyin da zasu bi wajen girke dakaru a kasar Guinea Bissau da Mali.

Taron shugabannin kasashen Kungiyar ECOWAS bayan kammala taro a Dakar kasar Senegal game da rikicin siyasar Mali da Guine Bissau
Taron shugabannin kasashen Kungiyar ECOWAS bayan kammala taro a Dakar kasar Senegal game da rikicin siyasar Mali da Guine Bissau AFP PHOTO / Seyllou
Talla

Taron na zuwa ne bayan amincewar shugabanin kasashensu, kan yadda za’a kawar da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar, bayan duk wani yunkuri na ganin sun mika mulki ya ci tura.

Kungiyar ECOWAS ta bukaci mika mulki ga shugaban Majalisar Dokokin Mali bayan hambarar da gwamnatin Amadou Toumani Toure a ranar 22 ga watan Maris.

A watan jiya ne Jagoran juyin mulki a Mali Kaftin Amadou Sanogo ya amince da bukatar ECOWAS game da kafa gwamnatin Rikon kwarya, kodayake ya mika mulki amma har yanzu shi ne jagoran tafiyar da kasar tare da bijerewa bukatar ECOWAS na gudanar da zabe cikin watanni 12.

A daya bangaren kuma a ranar Jum’a ne Sojojin Guinea Bissau suka amince Manuel Serifo Nhamadjo kakakin Majalisar kasar ya jagoranci gwamnatin rikon kwarya

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.