Isa ga babban shafi
Najeriya

Bama bamai sun tashi a Kaduna da Abuja a ginin Jaridar This Day

An samu tashin bom a ginin Kamfanin Jaridar This Day a birnin Abuja bayan wani Bom ya tashi a Kaduna kusa da Ofishin Jaridar a kan titin Kontagora. Jami’an tsaro sun ce an cafke wani mutum da ake zargin ya dala Bom a Kaduna.

Harin Ginin Kamfanin Jaridar this Day a Abuja Najeriya
Harin Ginin Kamfanin Jaridar this Day a Abuja Najeriya Premium Times
Talla

Har yanzu bubu wani cikakken bayani game da bama bamai, sai dai rehotanni sun ce mutane uku sun mutu a harin Abuja wasu uku kuma suka mutu a Kaduna amma Wakilin Rfi a Kaduna yace babu mutuwa amma an samu mutane da dama da suka samu rauni.

Hukumar Agajin gaggawa ta NEMA tace akwai mutanen da aka kwasa zuwa Asibiti a Abuja. Kuma hukumar tace an dasa Bom din ne a cikin harabar ginin This Day.

Yusha’u Shuaib Jami’in hukumar NEMA yace har yanzu babu wani labari game da adadin wadanda suka mutu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.