Isa ga babban shafi
Senegal

Macky Sall ya karbi rantsuwar shugabancin Senegal

Zababben shugaban kasar Senegal, Macky Sall ya karbi rantsuwar kama aiki, wanda ya kada Abdullahi Wade a zaben shugaban kasa. Shugabanin kasashe da dama ne suka halarci bukin rantsar da sabon shugaban.

Macky Sall. Zababben Shugaban kasar Senegal wanda ya kada Abdoulaye Wade a zaben shugaban kasa
Macky Sall. Zababben Shugaban kasar Senegal wanda ya kada Abdoulaye Wade a zaben shugaban kasa AFP PHOTO/ SEYLLOU
Talla

Macky Sally ya smau rinjaye kuri’u kashi 65.8 a zaben day a ba shi nasarar kada Abdoulaye Wade wanda ya yi yunkurin yin tazarce wa’adi na uku.

Mista Sall, ya kasance Shugaba na hudu da zai jagoranci kasar Senegal, kasar da bata taba ganin mulkin soji ba.

Sall mai shekaru 50 na haihuwa wanda tsohon Fira Minista ne, zai kasance shugaba na farko da aka Haifa bayan samun ‘Yancin kasar.

A lokacin bukin rantsar da Macky Sall ne shugabannin kasashen Afrika zasu gana game da juyin mulkin kasar Mali bayan Sojoji sun hambarar da gwamnatin Toumani Toure.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.