Isa ga babban shafi
Mali

Kasashen Duniya sun yi Allah waddai da juyin mulkin Mali

Kasashen Duniya na ci gaba da tir tare da Allah wadai, da juyin mulkin da Sojoji suka yi a kasar Mali wadanda suka hambarar da gwamnatin Amadou Toumani Toure tare da dakatakar da kundin tsarin mulkin kasar.

Sojin kasar Mali a lokacin da suke bada sanarwar karbe madafan ikon Mali ta kafar Telebijin a kasar
Sojin kasar Mali a lokacin da suke bada sanarwar karbe madafan ikon Mali ta kafar Telebijin a kasar REUTERS/Mali TV
Talla

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS/CEDEAO, da kungiyar Tarayyar Turai sun nuna bakin ciki da abunda ya faru. Yayin da Bankin Duniya da Bankin Raya kasashen Afrika suka dakatar da wakilcin kasar.

Bayan karbe fadar Shugaban kasa, Babu tabbacin inda hambararren Shugaba Toumani Toure yake yanzu haka.

Sojojin kasar karkashin Kaftin Amadou Haya Sanogo ne suka kifar da gwamnati tare da rufe iyakokin kasar.

Shugaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya Mark Lyall Grant ya bayyana cewa Mambobin kasashen Majalisar sun yi kakkausar suka da kwace madafan iko daga zababbiyar gwamnatin kasar Mali da sojoji suka yi tare da kira ga sojin su tabbatar da tsaron lafiyar Shugaba Amadou Toumani Toure, kuma su koma bariki.

A jiya alhamis ne Sojojin kasar Mali suka kifar da gwamnatin kasar, juyin mulki na tun bayan shekaru 21.

Kasar Faransa da ta reni Mali ta kaste duk wata hulda da kasar tare da kiran Sojin kasar kare lafiyar shugaba Toure.

Sojin kasar dai sun sun hambarar da gwamnatin ne saboda halin da kasar ta shiga na matsalar tsaro tare da kokarin girka Demokaradiya mai dorewa a cikin kasar.

Sabuwar gwamnatin Sojin kasar Mali ta bukaci ma’aikata komawa aikinsu a ranar Talata makon gobe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.