Isa ga babban shafi
Senegal

Shugaban Senegal Wade ya amince wankin hula ya kai shi dare

Senegal kasar Senegal Abdoulaye Wade ya amince da cewa tabbata babu tantama za a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu, tsakanin shugaba Wade da Makky Sall, kamar yadda kashi 50 na sakamakon da aka bayar ya nuna.Papa Dieng, kakakin shugaba Abdoulaye Wade, ya ce zasu sake tsarin yakin neman zabe, da kuma tabatar da cewa, mutane sun kara fitowa domin samun nasara. 

Macky Sall da Abdoudlaye Wade zasu tafi zabe zagaye na biyu
Macky Sall da Abdoudlaye Wade zasu tafi zabe zagaye na biyu SEYLLOU / AFP
Talla

Zai yi wuya shugaba Wade ya tsallake gangamin da 'yan adawan kasar zasu shirya masa domin kawar da shi daga madafun iko bayan mulkin shekaru 12. Wade dan shekaru 85 da haihuwa ya lashe zaben shekara ta 2000, sakamakon gangamin da 'yan adawa suka yi, domin kawar da tsohuwar jam'iyya mai mulki. A wancan lokaci Wade ya shafe shekaru masu yawa yana adawa da gwamnatin kasar.

Jaridun Senegal sun mayar da hankali kan zabe
Jaridun Senegal sun mayar da hankali kan zabe Reuters/Youssef Boudlal

Mutumin da ya zo na biyu Macky Sall, dan shekaru 50 da haihuwa, tsohon Fira Minista kuma masanin ma'adanai ya rike mukamai daban daban karkashin mulkin Wade, kafin su raba gari, ya kafa sabuwar jam'iyya. Kuma yanzu zai dogara da gangamin da 'yan adawa zasu yi domin tallafa masa kwace madafun iko daga wajen Wade, wanda yanzu haka ya ke fuskantar fushin 'yan kasar saboda tsawa kai da kafa ya yi takara karo na uku, duk da kyara da aka yiwa kundin tsarin mulki aka takaita wa'adin shugaba kasa shekaru biyar sau biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.