Isa ga babban shafi
Senegal

An Bude rufunan zaben kasar Senegal

Da safiyar yau Asabar al’umar kasar Senegal ke kada kuri’ar zaben sabon Shugaban kasa cikin yanayin rudani inda Shugaba Abdoulaye Wade ke takara karo na uku, dukda kyara da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar aka takaita wa’adi biyu na shekaru ga mukamun na shugaban kasa.

Reuters/Joe Penny
Talla

Akwai kimanin masu zabe milyan 5.3 tare da ‘yan takara 14 dake neman shugabancin kasar dake yankin Yammacin Afrika, wadda Faransa ta yi mata mulkin mallaka, kuma ta shafe shekaru tun bayan samun ‘yanci a shekarar 1960 da kwanciyar hankali ta bangaren siyasa.

Babban jami’an MDD Ban Ki-moon ya nuna damuwa da halin da ake ciki a kasar Senegal, yayin da ake shirin gudanar da zaben Shugaban kasar.

Ban ya nemi ganin zaben ya gudana cikin gaskiya da adalci, yayin da ya kai ziyara zuwa Lusaka babban birnin kasar Zambia.

Takarar Shugaba Abdoulaye Wade karo na uku, ta zama abunda ke haifar da rikici cikin kasar data dade cikin kwanciyar hankalin siyasa.

Akalla mutane shida sun hallaka cikin artabu da jami’an tsaron kasra ta Senegal, yayin gangamin nuna adawa da shirin Shugaba Wade na sake takara karo na uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.